Home

Music

Video

Kanny

Tags:

Tirkashi: Zpretty ta caccaki 'yan soshiyal midiya




Matashiyar jarumar masana’antar Kannywood , Zulaihat Ibrahim wacce aka fi sani da Zpretty ta caccaki ma’abota tsegumi a kafafen sada zumuntar zamani
- Jarumar ta wallafa bidiyo a shafinta na Instagram ne inda ta ke magana a kan masu bata wa jaruman masana’antar suna
- Ta yi gargadin cewa, zata iya daukar mataki a kan duk wanda ta kama da laifin bibiyar lamurranta tare da bata mata suna
Matashiyar jarumar masana’antar Kannywood, Zulaihat Ibrahim wacce aka fi sani da Zpretty ta caccaki ma’abota amfani da kafafen sadarwa ta zamani.


A wani bidiyo da jarumar ta wallafa a shafinta na Instagram, ta yi suka ga wadanda suka kware wajen bibiyar lamuranta da na sauran jarumai abokanan sana'arta. Wadanda daga zarar sun ga jarumi ko jaruma ta wallafa sabon hoto, zasu fara yadawa tare da tsokaci a kai.


Jarumar ta yi kausasan kalamai na musamman ga masu wallafa bayanai a dandalin YouTube, inda ta ce mafi yawansu basu da aikin yi face shirya karya da gulma, don batawa jaruman masana’antar Kannywood suna a idon duniya.

Jarumar ta yi wata barazana inda ta ke cewa, “Ku kiyaye ni, zan fa iya yin wani abu a kan duk wanda na samu da bibiyata ta irin wannan sigar” .
Kawo yanzu dai, sama da mutane dubu biyu ne suka kalli wannan bidiyon na jarumar. Sama da mutane dari kuwa sun yi tsokaci a kai.

Da yawa daga cikin jaruman masana’antar da suka yi tsokaci a kan gargadin, sun yi ta bata hakuri ne

Share this


0 komentar:

Post a Comment

Popular post

No.1 Nigerian Blog || Free Download | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Design By Hausazone Technologies