Home

Music

Video

Kanny

Tags:

'Kokarin kwaikwayon Turawa ya sa ake yawan sukar 'yan Kannywood'




Jama'a da dama na yawan sukar taurarin fina-finan Hausa wato Kannywood musamman a kafofin sada zumunta.
Akwai wasu daga cikin 'yan masana'antar Kannywood din da ba a cika sukar su ba, wadansu kuma a duk lokacin da suka yi magana, wasu kan yi kokarin sukar su.
BBC ta tattauna da Ibrahim Sheme, dan jarida ne kuma masani kan harkar fina-finan Hausa kan yadda yake kallon wannan lamari.

Ya bayyana cewa akasari caccakar da ake yi wa 'yan Kannywood na da alaka da irin sakonnin da suke wallafawa a shafukansu na sada zumunta, amma kuma a wani lokacin, akwai nau'in wasu mutane da ko wane irin sako suka wallafa sai sun caccaki 'yan Kannywood din, in ji Ibrahim Sheme.
Ya bayyana cewa ''akwai fadace-fadace da rigingimu da 'yan fim suka rinka shiga ciki wanda wannan ya ja musu bakin jini."
Sheme ya kuma ce a wani lokacin wasun su kan fadi wata magana wacce za ta jawo ce-ce-ku-ce wanda daga baya har ya ja a rinka zaginsu.

Har ila yau ya bayyana cewa "a shekarun baya ba a cika ganin 'yan fim cikin bainar jama'a ba, duk lokacin da aka gansu, jama'a kan kwadaitu domin musabaha da su, amma a halin yanzu saboda kafofin sada zumunta, sun kara matsowa kusa da mutane."

Ya ce ''bukukuwan Gala da ake yi a da, fitattun 'yan fim ba sa zuwa, amma a yanzu kusan dukansu suna zuwa.''
Hakazalika BBC ta samu tattaunawa da Aliyu Abdullahi Gora II, shi ma dan jarida ne kuma masani ne kan harkar fina-finan Hausa ya kuma bayyana cewa koyi da wasu daga cikin 'yan Kannywood suke yi da 'yan fim din kudanci na daga cikin abubuwan da ya sa ake sukarsu.

''Ya ce da karfi da yaji abin da 'yan fina-finan kudanci da Turawa suka yi sai su ce shi za su yi dole, babu yadda za a yi su zo arewacin Najeriya su yi irin haka sannan mutane su zuba musu ido.''

Ya kuma soki shugabancin Kannywood inda ya bayyana cewa shugabanninsu ''sun kaskantar da kawunansu'' ba su tsawata wa 'yan fim idan sun yi wani laifi.
Aliyu Gora ya gasgata irin kalaman da Ibrahim Sheme ya yi inda shi ma ya ce ''irin yadda suke tona wa juna asiri a kafofin sada zumunta ya sa mutuncinsu ke zubewa.''

A nasa bangaren, Ibrahim Sheme ya kara da cewa wasu daga cikinsu na saka irin tufafin da bai dace ba su dauki hoto kuma su saka hotunan a kafafen sada zumunta.
Wasu daga cikin abubuwan da suka jawo ce-ce-ku-ce a Kannywood
Na baya-bayan nan shi ne hoton su Hadiza Gabon da Rahama Sadau da Fati Washa wanda suka sa a karshen makon da ya gabata, kuma sun dauke shi ne a birnin Landan.

Hoton ya jawo ce-ce ku ce da suka sosai al'amarin da ya sa har jaruman suka gaza hakuri suka tanka, daga baya kuma aka ga Gabon ta zo ta yi da na sanin tankiyar har ma ta nemi gafarar Allah SWT.

Fati Washa na daya daga cikin 'yan Kannywood din da ke shan suka idan suka saka hoto ko kuma suka yi wata magana duk da cewa a wani lokacin akwai wasu masu yabonsu.

A lokacin da ta saka wannan hoton na sama wato ranar 1 ga watan Oktoba, wato ranar da Najeriya ta cika shekara 59, Fati ta sanya koriyar rigar 'yan kwallo da farin mayafi mai alamar tutar Najeriya kuma ta daga kanta sama tana dariya.

Wannan hoton ya janyo ce-ce-ku-ce inda wasu suka rika sukar yanayin shigar suna ganin cewa surar jikinta ta bayyana.
Wata mai amfani da shafin mai suna @alimikeh ta ce "Gaskiya wannan rigar ba ta dace ba duk surar kirjinki ta bayyana."
Yayin da @b.simoli ya ce "Adai tuna cewa akwai MUTUWA."
Wasu masu amfani da shafin na Instagram kuwa sun bar wa jarumar sakonni na kambamawa da yabo a karkashin hoton.
Rahama Sadau
A shekarun baya, tauraruwar fina-finan Hausa Rahama Sadau ta sha suka musamman a kafofin sada zumunta sakamakon rungumar mawakin nan, Classiq da ta yi.

Wannan ya jawo suka matuka ga Rahama Sadau da Kannywood baki daya, inda akasarin jama'a ke nuna cewa abin da ta yi ya saba wa addininta da kuma al'adar Bahaushe.

Wannan ne ya ja har hukumar da ke sa ido kan tace fina-finai ta dakatar da ita duk da cewa wasu sun yi korafi kan cewa wasu 'yan wasan sun yi abin da ya fi na Rahama, kuma ba a dauki mataki a kansu ba.
Nafisa Abdullahi wadda aka fi sani da ''Nafisa Sai Wata Rana'' na daya daga cikin wadanda ke shan suka a duk lokacin da suka saka wani hoto da wasu ke ganin bai dace ba a shafukan sada zumunta.
Misali a wannan hoton na sama da ta saka, daruruwan mutane ne suka yi magana a kai, amma da dama daga cikinsu suna sukarta dangane da kayan da ta saka.
Akwai @elsurajo_ wanda ya mayar mata da martani a shafin Twitter dangane da wannan hoton inda ya ce ''Ki ji Tsoron Allah ki tafi zuwa aure wallahi wannan ba ta hish-sheki.''

Sai kuma @TI___khalil, shi ma a shafin Twitter ya mayar mata da martani kan wannan hoto inda ya ce ''Gaskiya Nafisa ina sonki.''

Rikicin da ya faru tsakanin Adam Zango da Ali Nuhu a baya na daya daga cikin abubuwan da suka jawo aka rinka sukar taurarin biyu musamman a shafukan sada zumunta.

A lokuta da dama sai rikicin da ke tsakaninsu ya lafa sai kuma ya dawo, wanda hakan ya janyo aka rinka caccakar su.

Sai dai zuwa yanzu, da alama jaruman biyu sun samu daidaito a tsakaninsu sakamakon an kwana biyu ba a ji suna rigima ba.
Sannan abin da ya bambanta sukar da ake musu da ta matan shi ne, su ba a cika sukarsu kan yanayin suturarsu ba sai dai kan rabuwar kansu.

Share this


0 komentar:

Post a Comment

Popular post

No.1 Nigerian Blog || Free Download | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Design By Hausazone Technologies