Home

Music

Video

Kanny

Tags:

Harkar fim ce ta sani nake yin shigar mutunci a gari - Fati Shu'uma

Daya daga cikin fitattun jarumai mata da suke tashe a wannan lokacin, Fati Shu’uma, ta bayyana yadda harkar fim ta canza mata rayuwarta

- Ta bayyana cewa, fim ya taimaka wa rayuwarta , ta yadda ko fita za ta yi sai ta yi shiga ta mutunci

- Jarumar ta bukaci addu’ar masoyanta a kan cikar burinta na samun miji nagari wanda zasu zauna lafiya tare da fahimta juna


Daya daga cikin fitattun jarumai mata da suke jan zarensu a masana’antar fina-finai ta Kannywood, Fati Abubakar, wacce aka fi sani da Fati Shu’uma, ta bayyana harkar fim a matsayin wata harka wacce ta sauya mata rayuwa ta zama wata ta daban.

Wanda da kamar ba a harkar fim take ba, da zai kasance ba haka lamarin yake ba.
Jarumar ta fadi haka ne a lokacin tattaunawarta da jaridar dimokaradiyya dangane da halin da ta samu kanta a a cikin masana’antar ta Kannywood.


Jarumar tace: “Gaskiya na samu sauyin rayuwa, wanda da kamar ba fim nake ba to hakan ba zai kasance a gareni ba, don ka ga zan iya shiga ko ina kuma in yi ma’amala da jama’a. Amma yanzu duk inda na je sai a rika nuna ni. Don haka idan zan fita ma wani lokaci sai na saka niqabi.”
“Kuma fim ya taimakawa rayuwata, ta yadda idan zan fita dole sai nayi shigar mutunci don kada a zageni. Kaga ai na yi sa'ar shi’ga harkar fim kuma ya gyara min rayuwata.”
Jaridar ta tambayeta, ko ta taba samun matsala dangane da shigar ta harkar fim? Sai ta ce, “Eh, zan iya cewa na samu matsala, domin tun da zan shigo, lokacin zan je in ga yadda ake yin fim din ‘Gani ga ka’ Sai kanin mahaifiyata ya dinga yi min fada. Kun san dai yadda mutane suke daukar harkar fim.

A tunaninsa zanje in tare a gidan
karuwai ne in zauna, amma daga baya, sai ya fahimta ya barni.”
Da aka tambayi jarumar ko me ya fi birgeta a harkar fim? Sai cewa tayi, “Abinda ya fi birgeni shine yadda nake gudanar da rayuwata cikin sauki. Rayuwata mai sauki ce. Bai wuce watanni biyu da shigowata masana’antar ba aka yi min fim dina wanda na fito a tauraruwar fim din.

Wannan kuwa ya sa an sanni, duk inda na shiga sai kaji ana kiran Fati Shu’uma.”
Ta bayyana babban burinta a yanzu bai wuce ta samu miji ta yi aure ba. Don haka ne take ta addu’ar Allah ya kawo mata miji nagari wanda zai fahimceta kuma su zauna lafiya har abada. Ta mika fatan alhairi ga masoyanta tare da barar addu’arsu don cikar burinta.

legit Hausa

Share this


0 komentar:

Post a Comment

Popular post

No.1 Nigerian Blog || Free Download | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Design By Hausazone Technologies