A kwanannan ne rahotanni ke fito wa daga karamar hukumar mulki ta KoKo-Besse da ke a cikin jihar Kebbi cewa, “An samu labarin garin wasu giwaye a fadamar garin Zariyar Kalakale, inda daga nan ne jama’ar yankin suka fara tattaki zuwa cikin fadamar garin nasu domin gane wa idanun su wadannan giwayen da suka shigo cikin yankin nasu.
Bayan jama’ar garin na Zariyar Kalakala sun ganar wa idonun su wadannan giwayen sai labari ya fara zagayawa cikin al’ummar jihar da kewayenta. Haka kuma shuwagabannin karamar hukumar da kuma sarakunan gargajiya na yankin suka samu wannan labarin ganin giwaye a yankinsu, daga nan ne shuwabannin suka sanar da gwamnatin jihar ta hannun kwamishinan ma’aikatar kula da muhalli ta jihar, Alhaji Musa Hassan Kalgo wanda a nan take ma’aikatar sa ta dauki matakin sanar da Gwamnan jihar, Sanata Abubakar Atiku Bagudu domin daukar matakin sanar da hukumomin da abin ya shafa na jihar da kuma na gwamnatin tarayya.
Haka kuma kafin Gwamnan jihar ya kai ziyarar gani da ido an samu labarin cewa wadannan giwayen sun daga daga fadamar garin Zariyar kalakala zuwa gonakin garin Ganten Fadama, saboda haka sai kuma labari ya kawo ga Gwamna Bagudu cewa “Giwayen sun daga daga fadamar ta Zariyar kalakala, sai ya yi kokarin sanin gaskiyar labarin da ya zo masa”. Inda ya shiga bincike kan bayyanan da ya samu ga hannun mukarabansa. Daga nan Gwamna ya nemi a bashi hotunan giwayen domin zama karin sheda kan cewa an gan giwaye a jihar sa ta Kebbi, bisa ga bayyanan da ya tantance gaskiyar su sai ya sanar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma nuna masa hotunan giwayen da aka gani a jihar da kuma gaya masa irin kokarin da jama’ar jihar su kayi wurin tabbatar da cewa an kare rayuwar dabbobin da kuma kula dasu batare da an kashe su ba, ko yi musu rauni a jikin su.
Har ilayau Gwamnan bai tsaya nan ba, ya kuma sheda wa mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbanjo kan ganin wadannan giwaye a jihar ta Kebbi, saboda haka shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma Mataimakinsa suka aike wa mutanen jihar ta Kebbi musamman garuruwan da aka ga wadannan giwayen sakon godiya da kuma jinjina ta musamman kan irin gagarumin kokarin da suka yi wurin ganin cewa sun kare rayiuwar giwayen da kuma sadaukar da kayan amfanin gonakin su ga wadannan dabbobin domin su ci a matsayin abincin su, wanda sakon godiyar da kuma jinjina ya biyo ta hannu Gwamna jihar domin ya isar da sakon ga jama’ar sa kan namijin kokarin da suka yi ga wadannan giwayen da aka gani jihar a cikin makon da ya gabata. Saboda haka wannan ba karamin kokari ba ne.
Bugu da kari ya cewa “Shugaban kasa da mataimakin sa nai muku godiya ta musamman kan kokarin da kukayi kan ganin cewa wadannan giwayen sun rayu batare da wata matsala ba”.
Bayan dawowar Gwamnan Bagudu daga Abuja bai tsaya wata-wata ba ya yi tattaki zuwa karamar hukumar mulki ta Bagudo inda giwayen suka koma da zama bayan sun bar fadamar garin Zariyar kalakala da ke a karamar hukumar KoKo-Besse, inda aka gansu a fadamar gonakin garuruwan Ganten Fadama da kuma Ganten Tudu duk a Bagudo. Gwamnan Abubakar Atiku Bagudu ya isa garin na Ganten Fadama tare da tawagarsa domin ya gane wa idanun sa wadannan giwayen da aka gani a yanki na Bagudo, inda ya samu rakiyar shugaban karamar hukumar mulki ta Bagudo,
Tun farko Gwamna Bagudu ya bada umurnin a samar wa tawagar ‘yan jaridu motoci domin kashin farko na ‘yan jaridu sa fara isa wurin kafin isowarsa. Sabada ‘yan jaridun sawon farko sun kama hanya zuwa garin na Ganten Fadama kafin zuwa shi Gwamna Bagudu, inda kan hanyar su ta zuwa garin na Ganten Fadama saka tarar da babbar gadar Tugga ta shafe da ruwa sakamakon matsalar ambaliyar ruwa da ake fama da ita a jihar ta kebbi, inda matasan yankin na Tugga ke amfani da damar ambaliyar ruwa domin mayar da gadar Tugga wata kasuwar samun kudi ta hanyar daurawa motocin da zasu wace yagiya domin fitar dasu cikin ruwa da suka shafe babbar hanyar mota da ta tashi tun daga garin Birnin-kebbi har zuwa kasashen janhuriyar Nijar da kuma Benin da suka yi iyaka da karamar hukumar mulki ta Bagudo da kuma karamar hukumar Dandi a jihar ta keebi , wanda motar ta ‘yan jarida ta kwashe kimanin sa’o’i talatin cikin ruwa kafin matasan suka fitar da motar cikin ruwa na kogin kwara da yashafe hanyar wadda malakar gwamnatin taraiya ce. Bayan an fitar da motar daga cikin ruwan kigin sai suka kama hanya har zuwa garin na Ganten Tudu domin gano inda giwayen biyu suke, wanda daga garin na Tugga zuwa Ganten Tudu sun share kimanin kilo mita goma shabiyar kafin suka iso Ganten Tudu. Haka kuma daga garin Gante ‘yan jarida sun dauki mashin-mashin zuwa cikin dajin fadamar Ganten Tudu inda giwayen biyu ke kiyo wanda tafiyar takai kilo mita uku daga nan ne tafiyar mashin-mashin ta kare, sai daya daga cikin mutanen garin da ya jagorancin ‘yan jarida bayan sun kai karshen hanyar da mashin ke kaiwa, Malam Dantallo Gante ya farad a cewa” ‘yan jarida ku shirya zamu shiga ruwa wanda zamu yi tafiyar da takai kilo mita biyu zuwa uku a cikin ruwan gulbi kafin kaiwa inda giwayen suke”. Hakazalika ‘yan jaidar saboda sadaukar da kansu da kuma irin sha’awa da suke da ga aikin nasu na jarida suka amsa ma Malam Dantallo cewa “mun shirya mu shiga ruwan kogin domin yana daya daga cikin aikin mu na jarida da ake kira a turance “inbestigatibe journalism” wato binciken kan ayyukan aikin jarida”.
Daga nan sai aka shiga ruwan kogin domin tabbatar da cewa an gano inda wadannan giwaye biyu suke. Har ilayau tawagar ta ‘yan jarida sun fara iyo cikin ruwan kogin har tsawon kilo mita uku suna tafiya cikin ruwa kafin daga karshe suka gan giwa da diyar ta a tsallaken kogin ruwan wanda yana hannun riga da wata katafariyar gonar shinkafa da mutanen garin suka cewa mallakar kanfani nan na shinkafar Labana da ke casar shinkafa a jihar kebbi. Tawagar ta ‘yan jarida daga Birnin-kebbi sun hada da wakilin gidan Radiyon na muryar Najeriya wato BOA Abubakar Malami Bagudo, wakilin gidan Talabijin na kasa reshin jihar kebbi, Usman Abdullahi Shehu, wakillan kamfanin Dillancin Labaru na kasar Najeriya wato NAN, Ibrahim Bello da Zubairu Tatu da kuma wakilin jaridar LEADERSHIP A Yau Umar Faruk da wakilin jaridar Daily Trust Ismail Adebayo.
Sauran sun hada da wakilin gidan Talabijin na jihar kebbi Muhammadu Yusuf, shugaban masu hoto na fadar gwamnatin jihar ta kebbi Shekare Ladan Kalgo, wakilin gidan Radiyon jihar kebbi Abu Sifiyanu, sai mai baiwa Gwamnan jihar Shawara kan kafar sada zumunta na social media Hajiya Aisha Augie tare da tawagar ta da kuma direban na ‘yan jarida Malam Badamasi Malami wanda ya yi kokarin sa na ganin cewa ya tuka motar ta ‘yan jarida zuwa da kuma dawowa. Bugu da kari bayan ‘yan jarida sun gan giwar da diyar ta sai suka dauki hotona da kuma jin ta bakin wasu daga cikin mutanen garin kan zuwan giwar a garin nasu.
Daga karshe Gwamnan jihar kebbi, Abubakar Atiku Bagudu ya bayyana jindadinsa ga tawagar ‘yan jaridar da suka gudanar da bincike kan inda giwayen suka bisa ga umurnin gwamnatin jihar da kuma taimakon ta domin ganin cewa ‘yan jarda sun gano inda giwayen su a dajin garin na Ganten Tudu da ke karamar hukumar mulki ta Bagudo. Ya kuma cewa “ gwamnatinsa a shirya take na tabbatar da cewa ta samar da kyakyawan tsaro da kuma kare lafiyar wadannan giwayen”, haka kuma ya kara da cewa duk hukumomin da ke da alhaki kan harakar dabbobin daji ya sanar dasu domin su shigo cikin domin bada shawara kan yadda za’a kula da wadannan giwayen”.
0 komentar:
Post a Comment