Wata ‘yar aiki mai shekaru 18 ta yi wa matar da ta ke yi wa aiki laga-laga, lamarin da ya sai da aka kwantar da ita a asibiti.
‘Yar aikin mai suna Susan Samson ta aikata wannan aika aika ne a ranar 5 ga watan nan a gidan matar da ke yankin Ejigbo a jahar Lagos.
Rahotanni sun bayyana cewa yanzu haka matar mai suna Mistura na kwance a asibitin koyarwa da ke jahar Lagos.
Jaridar Puch ta rahoto cewa Mistura wacce ma’aikaciyar gwamnati ce ta dauki Samson aiki ta wani kamfani a ranar 4 ga watan Fabrilun shekarar nan domin ta taimaka mata da ayyukan gida.
Toh sai a ranar Juma’ar da ta gabata, Samson ta saci kudaden Mistura, kuma Mistura ta gansu a cikin kajar ta, kamar yadda rahotan ya bayyana.
A sakamakon haka ne Mistura ta kira kamfanin da ke wikiltar Samson tare da kulle gidan kafin su zo.
A yunkurin guduwa daga gidan ne Samson ta zubawa Mistura markadadden yaji yayin da ta ke kwance a kan gado, sannan ta dauki kwalba ta yi ta bugawa a kan ta har ta sume.
Rahotan ya bayyana cewa makotan Mistura ne suka kama Samson a yayin da ta ke yunkurin guduwa, saboda sun ji Mistura na ihu.
Yanzu haka Samson na hannun jami’an ‘yan sandan yankin Ejigbo.
0 komentar:
Post a Comment