
Ko ka san cewa mutane na mutuwa a kullum sakamakon ciwon dajin mafitsara? Shin ka san ana yi wa mutum sama da dubu arba’in (40,000) aiki a kowace shekara a kan matsalar iwon dajin mafitsara kuwa? Wannan na nuna cewa, kullum ana yi wa sama da mutum dari(100) aiki a kan wannan cuta.
An yi hasashen cewa, nan da shekara ta 2030, ciwon dajinmafitsara ne zai fi kowane ciwo yawa a duniya. Domin kuwa hasashen ya nuna cewa, cikin kowadanne mutum takwas za a samu mutum daya da ke da wannan cuta. Kusan duk inda ka ji wani ya mutu a Nijeriya, za ka ji an ce ciwon dajin mafitsara ne ya yi sanadiyyar rasuwarsa. Ciwon ya fi shafar manyan mutane wadanda shekarunsu suka kama daga 72 zuwa sama.
Kodayake ba mu da kididdigar mutanen da ke mutuwa ko ke kamu wa da wannan ciwo wanda ke da hanyoyin samun kariya a Nijeriya ba, amma za mu iya kwatanta wa daga kididdigar Amurka wadda ta yi wa ‘yan kasarta da ke zaune a Afirka masu shekara tsakanin 50 zuwa 54, saboda akwai kamance tsakaninmu da su.
A kasar Asiya kuwa, wanna ciwo bai yi karfi ba. Ba a san mene ne dalilin da ya sa aka samu bambanci ba wajen kamu wa da wannan ciwo a tsakanin mutanen da suke da bambancin launin fata ba, sai dai ana tsammanin kwayar halittar gado ce za ta zama sanadi.
Yanayin abinci na da muhimmanci wajen wancan kwatanta tsakanin ‘yan Nijeriya da ‘yan kasar Amurka mazauna Afirka, kamr irin su, wake da kuma cika mai a cikin abinci, saboda haka wannan ciwo wanda ake danganta shi da bakar fata wanda kuma ya kamata ‘yan Nijeriya su kiyaye.
Ciwon kansar mafitsarar na kama karkashin mafitsara, wanda ke kewaye da mafitsarar namiji. Ita ke samar da kwayoyin halittar da ke samar da maniyi, wanda daga nan ne maniyi ke fita bayan saduwa da mace.
Ciwon kansar mafitsara ciwo ne da manya ke yi, wadanda suka fara tsufa. Ya kamata mutumin da ya fara manyata ya lura da wadannan alamu, wadanda da zarar ya fara jinsu sai ya garzaya gurin likita.
Wahalar fitar fitsari: Ya kamata maza su lura da wannan sosai, musamman idan ana jin zafi a karshe fitsari. Ya kamata a je wajen likita, da zarar an ji wani canji wajen fitar fitsari, kamar haka:
Yawan yin fitsari, na daga cikin alamun ciwon kansar mafitsara. Wasu alamun kuma su ne:
Yawan yin fitsari da daddare.
Wahalar fitar fitsari.
Fitar fitsari a hankali.
Raguwar karfin fitar maniyi.
Yin fitsari da jini.
Abubuwan da ke kawo karuwar kansar mafitsara.
Tsufa ko rashin kwanciyar hankali ko shakar sinadarai masu karfi kamar a wajen aiki gurbataccen ruwa ko cin abincin da ya lalace, wadannan na daga cikin abubuwan da aka gano cewa ,suna haifar da ciwon kansar mafitsara.
Yawan kwayar halittar “prolactin” da ke cikin jini, na kara sinadarin da ke cikin mafitsara, wanda ke samar da sinadarin “Di-Hydro-testoterone”.
Yawan wannan sinadari na DHT a mafitsara zai iya kara girman mafitsara. Rashin kwanciyar hankali dag ado na daga cikin abubuwan da ke kawo cutar kansar mafitsara.
Sakamakon wani bincike ya tabbatar da cewa, idan wani daga cikin iyali na da ciwin kansar mafitsara, akwai hashen cewa daya daga cikin iyalin dole ya kasance ya kamu da wannan ciwo, saboda haka ne, ake ganin wannan ciwo nag a alaka da gado.
Yawan sa maganin kasha kwari a cikin kayan abincimumusamman wadanda za a ajiye su zuwa lokaci mai tsawo na haifar da irin wannan ciwo ga wadanda suka yi amfani da su.
Akwai sinadaran da ke cikin wasu abincinmu kamar irin su, ‘ya’yan itace da kayan lambu da manya-manyan kifaye duk suna daga cikin abubuwan da ke kawo irin wannan ciwo.
Bayan tsuke mafitsara, da rage yawan samar da maniyi, wadanda ke yawan saduwa da mata na da kasadar kamuwa da cutar kasar mafitsara.
Cin abinci mai maid a jan nama na kawo cutar kansar mafitsara kamar yadad shan taba ko giya ke haifar da wannan ciwo.
Taba na da wani sinadari da ke haduwa da yawu sais u haifar da wani sinadari da ke karfafa DHT, wajen kara mafitsara.
Giya ita ma tana kara yawan sinadarine “prolactin hormone”. Wannan shi kuma yana kara yawan sinadarin da ke mafitsara wanda kuma a karshe girmanta yake karuwa.
Yadda ake kare kai daga kamu wad a ciwon kansar mafitsara. Saurin zuwa wajen likita da zararar an ji alamun kamuwa da wannan ciwo zai taimaka wajen samun kariya daga cutar. Yanzu haka an gano wadnsu hanyoyi na gwaje-gwaje da za su nuna alamun cutar tun kafin su yi karfi.
Yawan sinadarin “PSA” na iya haifar da ciwon kasar mafitsara. Saboda haka ana shawartar jama’a da su dinga zuwa wajen likita a kalla duk shekara don ya san halin da yake ciki.
Ana shwartar maza su magungunan da kunshi da Bitamin C da D da E da kuma sinadari Zinc. Zinc yana muhimmanci, saboda yana taimaka wa wajen daidaita aikin mafitsara, yana kuma tace dukkan wani abu mai cutarwa ya fitar da shi. Binciken da aka yi ya nuna yin amfani kawayar magani mai sinadarin Zinc miligiram 150, a kowace rana na tsawon wata biyu da kuma shan kwayar miligiram 50 zuwa150 a kullum ya nuna nasaraar da aka samu ta 74 cikin dari na magance wannan matsala.
Masu fama da wannan ciwo na iya mafani da tumaturi da kankana wada ke dauke da sinadarin “Lycopene” domin samun sauki.Haka kuma tsofaffi za su iya bin hanyoyin da za su kare kansu daga kamu wa da wannan ciwo, ta hanyar rage cin abinci mai mai.
0 komentar:
Post a Comment