Home

Music

Video

Kanny

Tags:

PDP Ta Goyi Bayan Bayanin Bill Gates




Jiya ne jam’iyyar PDP ta ce bayanin da Bill Gates ya yi dangane da tsarin tattalin arzikin Buhari, ba wanda zai taimaka ma talakawa ba, magana ce ta gaskiya, shi ya sa ma ‘yan Nijeriya suka shirya korar APC a zaben shekarata 2019.

Jam’iyyar ta ce wannan maganar da attajiri Bill Gates ya furta, ya nuna cewar mulkin shugaban kasa Buhari, shi ne wanda al’ummar Nijeriya suka fi shan wahala a tarihin kasar Nijeriya, wannan kuma ya nuna ba a tare da ‘yan Nijeriya.

Wannan bayanin ya fito ne daga bakin Sakataren ayar da kan jama’a na kasa, Kola Ologbondiyan wnda ya ce, shugaban kasa Buhari da kuma jam’iyyar APC za su gane cewar yanzu duniya ta gane, irin salon mulkin da Buhari ya ke, wanda ana bata dukiyar kasa ne, da kuma neman a sake yardaa zabe shi.

Jam’iyyar cewa tayi ita tana ma ganin shi Bill Gates ya dan yi sassauci akan tsarin tattalin arzikin shugaban kasa Buhari.
Ya kara bayanin ‘’ Abin da Bil Gates bai fadi ma Buhari da ‘yan tawagar shi shi ne, mulkinsu ya gaza, ya rasa abin da yake ciki, da kuma rudewa, har ma rasa yadda tsara shirin tattalin arziki wanda ya sa kasa ta shiga halin kaka nika yi.’’

‘’Maganar da Bill Gates ya yi dangane tsarin tattalin arziki na shugaban kasa Buhari, a kuma fadar shugaban kasa, gaban kuma mataimakin shi Farfesa Yemi Osinbanjo, ya zo ma shugaban kasa Buhari da kuma ita jam’iyyar APC, saboda sun so su yi amfani da damar ce, wajen maganar zaben shekarar ta 2019.
‘Wani babban abin takaici shi ne maimakon ita jam’iyyar APC da shi Farfesa Osinbanjo su nuna nadama akan abin da suka yi ma’yan Nijeriya sai suka nuna kamar an yi masu kage ne, bayan kuma ga hujjoji.

‘’Duniya ta nuna bata ji dadi ba, saboda a karkashin mulkin a karkashin mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma APC, wannan babbar kasa tamu wadda a da can take da tattalin arziki mai karfi,yanzu ta koma kasar da akai matsala matar mutumta haihu,saboda ita ce ta hudu a wajen yawan mutuwar kananan yara a duniya.

‘’A cikin shekaru uku da suka wuce wannan mulki ya kasa bullo da wani tsari wanda zai yi aiki sosai, a kan harkar lafiya, ilmi, harkar gidaje, wutar lantarki, ci gaban masana’antu, babban tafarkin tattalin arziki, samar da ayyukan yi, ko kumawani tsari wanda tsari mafi dacewa saboda talakawan kasa.

‘’Maimakon haka abin da’yan Nijeriya suka samu shi ne tattalin arziki wanda bai da alkibla, ga kuma karin kudaden haraji,suma kayayyakin masarufi basu tsira ba dangane da harajin, kayayyakin abinci an kara masu farashi tare da manfetur, ga kuma tulin bashin kasashen waje, da dai sauransu.

‘’Watakila dai wannan mulki yana jin dadi ganin’yan Nijeriya suna shan wahala, akan yunwa, da halin kunci,duk kuwa da yake muna abubuwan da bai kamata ace an shiga wannan halin matsin ba.

‘’Duk da haka muna kira ga ‘yan Nijeriya da kada su damu su kuma kara hakuri, da yake muna cikin kao gyare gyare a jam’iyyarmu, da kuma dan takararmu mai son jama’a, za mu yi kokari mu kwato ma ‘yan Nijeiya ‘yancinsu shekara ta 2019.’’

Share this


0 komentar:

Post a Comment

Popular post

No.1 Nigerian Blog || Free Download | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Design By Hausazone Technologies