Home

Music

Video

Kanny

Tags:

‘Ina Yawan Rashin Lafiya Sakamakon Kaurace Min Da Mijina Ya Ke Yi’ – Bilkisu Azeez



Rahotanni sun bayyana cewa wata matar aure mai shekaru 35 mai suna Bilkisu Azeez da ke zaune a unguwar Igando a jihar Legas ta maka mijinta a kotu sanadiyyar kaurace mata da yake yi.

Bilikisu wacce ‘yar kasuwa ce ta roki kotun da ta warware aurenta da mijinta saboda kaurace mata da yake inda hakan ke sa ta rashin lafiya.

Kwanciyar da nayi na karshe a asibiti kafin na zo kotu likita ya fada min cewa rashin saduwa ne da mijina akai-akai ya kawo mun rashin lafiya.

Bilkisu ta zargi mijinta da cewa tun da ya yi sabuwar amarya ne ya kaurace mata sannan ya yi watsi da kula da dansu daya namiji da suka haifa.

Olushesi ya kan lakada mun duka saboda amaryar sa sannan daga ni har dan yaro na bamu tsira daga masifar wannan amarya ba.
Bayan haka Olushesi ya ce tabas ya kauracewa Bilikisu amma ya yi haka ne saboda ramakon kaurace masa da ta fara yi.

“Ranar da Bilkisu ta fara kaurace mini babu irin juyin duniyan nan da ban yi ba ta amince da ni amma ta ki sai dai ta tashi daga kan gadon ta yi shinfida a kasa ta kwanta”
Alkalin kotun Akin Akinniyi ya daga cigaba da shari’ar zuwa ranar 12 ga watan Afirilu.

Share this


0 komentar:

Post a Comment

Popular post

No.1 Nigerian Blog || Free Download | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Design By Hausazone Technologies