Home

Music

Video

Kanny

Tags:

Dalilin Da Yasa Nayi Aure Sau Bakwai (7) Inji Sadiya Kabala



Jarumar Finafinan Hausa Sadiya Kabala, ta bayyana cewa abin da yasa ta yi aure sau 7 a cikin fim din 'Kwadayi da Buri' domin ta nuna illar son abin duniya ga 'yan matan wannan zamanin.

Jarumar, wadda ta fito da sunan Salmah a fim din, ta yi aure barkatai sakamakon kawayen banza, da ta ke dasu wadanda suka rika bata mummunar shawara.

A cewar ta abin da yasa ta fito da wannan halin, domin ta nunawa masu wannan burin a zuciyar su cewa shi fa kwadayi mabudin wahala ne, kuma da mai kudi da talaka, dukansu Allah ya yi su, Allah zai iya azurta wanda yaso a lokacin da ya ga dama, kuma zai iya talauta wanda yaso a lokacin da ya ga dama.
Daga karshe ta shawarci 'yan uwanta mata da su zamo mutane na gari.


Share this


0 komentar:

Post a Comment

Popular post

No.1 Nigerian Blog || Free Download | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Design By Hausazone Technologies