Home

Music

Video

Kanny

Tags:

Kotu Ta Garkame Malamin Da Ya Yiwa Dalibarsa ‘Yar Shekaru 14 Fyade




Wata Kutun majistare da ke birnin Damaturu a jihar Yobe ta yankewa wani malamin makaranta hukuncin dauren shekaru 10 bayan ta kama shi da laifin yiwa wata dalibarsa ‘yar shekaru 14 fyade.

Rahotanni daga kafafen yada labarai na Daily Trust ta bayyana suna wanda aka yankewa hukuncin a matsayin, Saleh Abdullahi, wanda ya kasance malamin makarantan sakandaren mata zalla ne wato Government Secondary School wanda ke Ngelzarma, a jihar Yobe.


A hukuncinsa, alkalin kotun, majisatre Abubakar Lamba Maluri, ya bayyana wanda ya aikata maifin a matsayin mutumin mara zurfin tunani, inda ya kara da cewa kotun zata tsaya tsaye wajen kare hakkin dalibai mata.
“Malaman makaranta ya kamata su kasance kamar iyaye ne a wurin dalibansu mata ba kamar abunda suka mallaka ba. Hukuncin da kotun ta yanke a kan wanda ake zargi ya zama gargadi ga sauran al’umma,” inji alkalin kotun.


Ya kuma yanke hukuncin dauren shekaru 10 a gidan yari ba tae da biyan kudin diyya ba.
“Na umurci wanda ake zargi ya biya dalibar da ya yiwa fyade naira N100,000 a kan matsayin diyya. Idan ya kasa biya, za’a kara masa shekaru 5 daga cikin shekaru 10 da kotu ta yanke masa a gidan yari.

“Na kuma umurci makarantar da ta amince da komawar dalibar a cikin kwanaki 14 don ta ci gaba da karantunta. Za a mika wannan umurnin zuwa ga shugaban makaranta, sannan kuma shi shugaban makarantar zai sanar da magatakardan wannan kotun a kan komawarta makarantar a cikin kwanakin 15,” alkalin kotun ya kara da cewa.

Lauyar da ya mika karar wanda ake ta saurararta a kotu na tsawon shekaru 1 kenan, ya ce wanda ake zargi ya kira dalibar zuwa dakin gwaje-gwaje na ilimin sunadarai wato Chemistry a kan cewa mahaifiyarta ta ba shi sako ya ba ta; a nan ne yayi amfani da iya karfensa wajen yi mata fyade.

Shaida na 5 da aka gabatar a gaban kotu a kan karar, Dr, Babagana Kolo, wanda ya duba dalibar da aka yiwa fyade a asibitin Maryam Abacha da ke birnin Damaturu, ya fadawa kotu cewa a binciken da yayi ya gano cewa yarinyar ta samu rauni a al’aurarta wanda hakan ya nuna cewa babu shakka an yi amfani da karfi wajen yin lalata da ita.

Share this


0 komentar:

Post a Comment

Popular post

No.1 Nigerian Blog || Free Download | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Design By Hausazone Technologies