Home

Music

Video

Kanny

Tags:

Dandalin Kannywood: Manyan matsaloli 2 da ke damun Rahma Sadau - Ali Nuhu



Kuruciya tare da daukaka ce ke damun Rahma Sadau - Ali Nuhu

- Ali Nuhu ya bayyana hakan ne a yayin da yake bayanin dalilin da yasa yake ta kokarin a maido da jarumar

- Yace zargin da ake yi masa na cewa ko yana so a maido da ita ne domin ya saka ta a cikin fim karya ne

Babban jarumin nan a masana'antar Kannywood watau Ali Nuhu ya bayyana jaruma Rahma Sadau a matsayin wadda kuruciya da kuma daukaka ke matukar damu inda kuma ya bukaci masu ruwa da tsaki a harkar fim din Hausa da suyi mata uzuri.

Jarumi Ali Nuhu ya bayyana hakan ne a yayin da yake bayar da ba'asi game da muhimmin dalilin da yasa yake ta kokarin a maido da jarumar a masana'antar bayan korar ta da aka yi.

NAIJ.com ta samu dai cewa Ali Nuhu ya kara da cewa, shi dai a iya sanin da yayi wa jarumar ba lallai bane ta kara aikata laifin da ta aikata don kuwa kullum ai dan adam na kara girma ne kuma hankali na kara shigar sa.
Haka zalika jarumin ya bayyana cewa zargin da ake yi masa na cewa ko yana so a maido da ita ne domin ya saka ta a cikin fim din sa kanzon kurege ne kawai babu kamshin gaskiya a ciki.

Share this


0 komentar:

Post a Comment

Popular post

No.1 Nigerian Blog || Free Download | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Design By Hausazone Technologies