Jaruma Fatima Abubakar wadda akafi sani da fati shu'uma ta bayyana cewa ba abunda bazata iya yi a film ba, acikin hirar da Jaridar blueprint tayi da ita, inda take cewa
"Idan za'a biya ni, ba irin fitowar da ba zanyi a film ba koda 'sex scene' ne amma sai da babban jarumi. Idan da babban jarumi ne 'I will not regret if I zip down'......." Inji Fati Shu'uma (mun saka wasu kalaman da turanci saboda bamu samu daidai dasu a yaren Hausa ba).
Sannan Jarumar ta Kannywood ta bayyana rashin jin dadi da bata samu muradin zuciyar ta ba wato shugaban Nigeria Muhammad Buhari.
Jarumar tana cewa "Ba wasa nake ba, ina so in auri shugaban kasan Nigeria wato Muhammad Buhari, yana da kyau da tsayi kuma sananne ne duk duniya sannan ga addini.
Duk da nasan matar sa tana da kyau zan aure shi in ya yarda. Ina rokon duk wanda yake kusa da shi da ya Isar min da sako"





0 komentar:
Post a Comment