Home

Music

Video

Kanny

Tags:

Ubangiji Ya Umarce Ni In Tsaya Takarar Shugaban Kasa - Fasto Tunde Bakare



Shugaban Cocin ' Latter Rain Assembly' wanda kuma ya yiwa Shugaba Buhari Mataimaki a takarar da suka yi a jam'iyyar CPC a 2011, Fasto Tunde Bakare ya yi ikirarin cewa Ubangiji ya umarce shi kan ya tsaya takarar shugabancin kasar nan a 2019.
Faston ya ce, tun da farko ya yi niyyar yin ritaya daga harkokin siyasa amma kuma Ubangiji ya sauya masa makomar rayuwa inda ya nuna cewa bai so bayyanawa duniya wannan al'amari ba don ya san za a caccake shi musamman magoya bayan Buhari wadanda ke ganin ya ci amanarsa a lokacin zaben 2011 a matsayin mataimakinsa.

Share this


0 komentar:

Post a Comment

Popular post

No.1 Nigerian Blog || Free Download | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Design By Hausazone Technologies