Home

Music

Video

Kanny

Tags:

Jawabin Shugaba Buhari Na Sabuwar Shekara A Takaice



Ina matukar bakin ciki kan yadda wasu tsirarun mutane suka hana al'ummar kasar nan samun walwala na bukukuwan Kirismeti da sabuwar shekara ta hanyar haddasa karancin fetur da gangan wanda hakan ya hana wasu samun yin tafiya zuwa garuruwansu saboda Tsadar kudin mota, don haka na yi alwashin hukunta wadannan tsirarun mutanen
> " Abu na biyu, Ina son sanar da ku irin matakan da gwamnati ke dauka kan inganta harkokin ci gaban kasa saboda muna shirin fadada ayyukan hanyoyin mota da na jiragen kasa da kuma harkar wutar lantarki. A game da harkar jiragen kasa, mun sanyawa kanmu wa'adi wanda tuni aikin gina hanyar jirgin kasa na Legas zuwa Kano ya rigaya ya yi nisa. " Muna sa ran kafin karshen shekarar 2019, aikin titin jirgin kasa sai kai garin Ibadan daga Legas
> " A game da ayyukan hanyoyi kuwa, an karfafa hukumar kula da hanyoyi ta kasa( FERMA), wadda aka dorawa nauyin yin gyara dukkanin hanyoyin da suka lalace a cikin makonni 12. Za a yi amfani da kudaden da aka samu ta hanyar tsarin, SUKUKU na Naira Bilyan 100 wajen aikin hanyoyi 25 da ke fadin kasar nan kamar haka:
a. Hanyar Oyo – Ogbomosho,
b. Hanyar Ofusu – Ore – Ajebandele – Shagamu,
c. Yenagoa Road Junction – Kolo Otuoke – Bayelsa Palm,
d. Enugu – Port Harcourt Dual Carriage Way,
e. Onitsha – Enugu Expressway,
f. Kaduna Eastern Bypass,
g. HanyarKano – Maiduguri
h. Hanyar Abuja – Lokoja – Benin
i. Hanyar Suleja – Minna
> " A game da harkar wutar lantarki kuwa, gwamnati ta bayar da Tallafin Naira bilya 701 ga kamfanonin da ke samar da hasken wutar lantarki don inganta ayyukansu. An kuma samu nasarar kammala ayyukan gyaran wasu tashoshin wutar lantarki wanda ya hada da na Afam, Katsina sai na Zungeru wanda aka kusa kammalawa. Sauran su ne, tashar Gurara, Kashimbala da na Mambila"
> " Game da tattalin arziki kuwa, za mu ci gaba da aiwatar da wasu tsare tsare na ganin an zaburar da tattalin arzikin kasa. A shekaru biyu da suka wuce, na nemi mutane su koma Gona kuma hakan ya fara tasiri saboda a cikin wannan shekara za mu dakatar da shigo da shinkafa gaba daya"
> " Ina sauraren muhawara da ake yi game da canjawa Nijeriya fasali sai dai abin sanin kawai shi ne, babu wani tsarin gwamnati da ba shi da ta sa matsala. Kasance kuma kakar siyasa za ta fara a cikin wannan, Ina kuma kira ga 'yan siyasa su guji amfani da kabilanci da addini wajen raba kan al'umma.

Share this


0 komentar:

Post a Comment

Popular post

No.1 Nigerian Blog || Free Download | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Design By Hausazone Technologies