Home

Music

Video

Kanny

Tags:

Ta Tsoma Hannun Dan Kishiyarta A Ruwan Zafi Saboda Ya Cinye Mata Abinci



Wata mata da aka bayyana sunanta a matsayin Khadija Adam ta illata dan kishiyarta dan shekara daya da wata shida da haihuwa ta hanyar tsoma hannunsa a ruwan zafi sakamakon cinye mata abinci da ya yi. Kamar yadda majiyarmu ta rawaito, lamarin ya auku ne a ranar Juma'ar da ta gabata a yankin Chukuku dake karamar hukumar Kuje a Abuja. Sannan majiyar ta mu ta kara da cewa, yaron wanda mahaifiyarsa ta tafi ta bar shi bayan samun sabani da mahaifinsa, tun daga wannan lokacin yana karkashin kulawar kishiyar mahaifiyar tasa ne wadda 'yar asalin jihar Kogi ne daga yankin Oboroke-Ebe-ba dake karamar hukumar Ihima Okehi.

Share this


0 komentar:

Post a Comment

Popular post

No.1 Nigerian Blog || Free Download | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Design By Hausazone Technologies