Home

Music

Video

Kanny

Tags:

Malaman addini suna samun salon wa'azi daga fina-finan hausa - Rashida Lobbo


Wata sabuwar jaruman Kannywood da ta wasu masu fashin baki suka ce ta shigo masana'antar da kafar dama tayi ikirarin cewa malaman addini suna samun salon yadda za su yi wa'azin su ne daga fina - finan hausa. Rashida Lobbo dai tana daya daga cikin jaruman da suka kyauta a bikin karama jaruman fim da mujalar city people ta shirya kwanakin baya a jihar Legas.

Rashida Lobbo wanda ake wa lakabi da yar Yola tana cikin sabbin jarumai da tauraron ke haskawa kuma da alama ta shirya damawa da sauran fitattun jarumai dake masana'antar cikin shekarar 2018 da zamu shiga.
Kamar yadda ta bayyana a shafin ta na sada zumunta na facebook, jarumar tana karkashin kamfanin shirya fina-fina na FKD wato mallakar shahararen jarumi, Ali Nuhu

Share this


0 komentar:

Post a Comment

Popular post

No.1 Nigerian Blog || Free Download | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Design By Hausazone Technologies