Home

Music

Video

Kanny

Tags:

Ina Kara Tunatar Da Buhari Da APC Kan Alkawuran Da Suka Daukarwa 'Yan Nijeriya, Inji Sheik Sani Yahaya Jingir



Kungiyar Izalatul Bidi’a wa Iqamatus Sunnah ta Kasa ta nemi Gwamnatin APC karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari ta cika alkawarin da ta dsukarwa 'yan Nijeriya a lokacin yakin neman zaben 2015. Shugaban majalisar Malamai na kungiyar Izala, Sheik Sani Yahaya Jingir ne ya bayyana hakan ne a wajen wani taron dalibai a wata kwalejin kiwon lafiya a garin Jos a shekaranjiya. Malamin ya ce Talakawa da kan su su ka rika kokarin ganin Buhari ya samu mulki. Kungiyar Musulunci ta yi kira ga Buhari da babban murya Kungiyar ta tunawa APC da alkawarun da ta yi wa ‘Yan Najeriya lokacin yakin neman zabe a 2015. Sheik Jingir ya tunatar da Gwamnatin Muhammadu Buhari irin alkawarin da ta dauka na gyara harkar ilmi, noma da ma gyara hanyoyi a Nijeriya. Bayan nan APC ta yi alkawarin kawo karshen rashin aikin yi har da ba masu zaman kawai N5000 duk wata. Haka Shehin Malamin ya yabawa Shugaba Buhari na kawo karshen ta’addanci da sata amma akwai sauran aiki wajen habaka tattalin arzikin kasar.

Share this


0 komentar:

Post a Comment

Popular post

No.1 Nigerian Blog || Free Download | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Design By Hausazone Technologies