Home

Music

Video

Kanny

Tags:

Dandalin Kannywood: Zaharaddeeni Sani ya tafi karo karatu a kasar Saudiyya


Daya daga cikin fitattun matasan jaruman nan a masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood watau Zaharadeeni Sani ya sanar da cewa yanzu haka yana fadada karatun sa ne a wata makaranta dake a garin Riyad can kasar Saudiyya.
Jarumin ya bayyana hakan ne a yayin da yake tattaunawa da majiyar mu ta mujallar Fim game da yadda ba'a ganin sa a fina-finai da yawa a halin yanzu.

Hausazone.Com ta samu cewa jarumin ya kuma bayyana cewa duk da hakan, yanzu haka yana nan akan shirya fim din sa mai suna 'Sangarta' a can kasar Saudiyya din.
Daga karshe sai kuma ya godewa masoyan sa da dukkan saunan masu bibiyar harkokin masana'antar ta sa sannan kuma ya sha alwashin cigaba da harkar fim din da zarar ya dawo gida Najeriya.

Share this


0 komentar:

Post a Comment

Popular post

No.1 Nigerian Blog || Free Download | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Design By Hausazone Technologies