Home

Music

Video

Kanny

Tags:

Dandalin Kannywood: Saratu Gidado Daso ta karyata zargi na mutuwar auren ta


Shahararriyar jaruman nan ta shirin wasan kwaikwayo na hausa, Saratu Gidado, wadda ta fi shahara da Daso, ta kore tuhumar jifa da wasu ke yi mata na mutuwar auren ta. Jarumar ta fina-finan Kannwood ta bayyana cewa, kamar yadda sauran gamagarin mata ke tinkaho da cewar su na da aure, haka itama take tutiya da kasancewar ta matar aure kuma ma'aikaciya.

Hajiya Daso tayi wannan batu ne domin karyata cecekuce na cewar auren ta ya mutu, inda take cewa har yanzu tana karkashin igiyar aure kuma tana zaune lafiya da mijin na ta.
Hausazone.com ta fahimci cewa, wanna sanarwar tazo ne da sanadin kamfanin jarida na Tozali, inda Daso take mayar da martani da masu yi mata kagen mutuwar auren ta.

Share this


0 komentar:

Post a Comment

Popular post

No.1 Nigerian Blog || Free Download | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Design By Hausazone Technologies