Home

Music

Video

Kanny

Tags:

Dandalin Kannywood: Mansura Isah ta hararowa mata ma'aurata bankayen dake cikin tsafta a gidajen aure


Fitacciyar jarumar nan ta shirin fina-finai na wasan hausa Mansura Isah, ta gargadi mata musamman ma'aurata akan tsaftace jikin su da kuma muhallan su a gidajen su na aure. Mansura wadda uwargida ce ga shahararren jarumin nan na Kannywood, Sani Musa Danja, tayi wannan jan hankali ne a wata ganawa da 'yan jarida na kamfanin Tozali, inda take baiwa mata shawarwari da kuma hararo musa amfanin tsafta a gidajen su na aure.

Jarumar ta nemi mata da su rika tsaftace jikin su wanda aikata hakan zai kara musu dankon soyayya tare da habakar sha'awar mazajen su a gare su.
Ta kuma nemi matan da su rungumi tsaftace muhallansu tare da wuraren su na zama tare da yin kwalliya da kuma ado ga mazajen su wajen yin amfani da kayan shafe-shafe kamar turare na jiki da na muhallai da su kara dankon soyayya a zukatan mazajen na su.

Share this


0 komentar:

Post a Comment

Popular post

No.1 Nigerian Blog || Free Download | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Design By Hausazone Technologies