Home

Music

Video

Kanny

Tags:

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad


Shararriyar jarumar nan ta Kannywood a masana'antar shirya fina-finan Hausa a zamanin da watau Fati Muhammad ta fito fili ta fara yi wa tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya Alhaji Atiku Abubakar kamfe. Jarumar dai kamar yadda muka samu daga wata majiyar da bamu tabbatar da sahihancin ta ba ta bayyana cewa ita a ra'ayin kanta tayi amannar cewa Atiku din shine kadai yake rike da mabudin ceton Najeriya daga halin da take ciki. Majiyarmu dai ta samu cewa a baya jarumar da ke 'yar asalin jihar Adamawa ta samu matsayi a cikin wata gidanuniyar ta Atiku inda ta zama shugaba a sashen arewacin Najeriya. Haka ma dai mai karatu zai iya tuna cewa a kwanan baya fitaccen dan siyasar ya sanar da ficewar sa daga jam'iyyar APC mai mulki inda ya koma jam'iyyar PDP ta adawa.

Share this


0 komentar:

Post a Comment

Popular post

No.1 Nigerian Blog || Free Download | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Design By Hausazone Technologies