Home

Music

Video

Kanny

Tags:

Dandalin Kannywood: Adam A. Zango yayi kaca-kaca da wadanda basu son Maulidi


Fitaccen jarumin nan, maishiryi, mai bayar da umurni da duniyar Kannywood sannan kuma shahararren mawaki ya fito ya bayyana matukar rashin jin dadin sa a kan abun da ya kira kushe da wasu suke yi masa wai don sun ganshi ya halarci taron maulidi. Jarumin dai yayi wannan kalamin ne a cikin wani faifan bidiyo da ya dauka sannan ya kuma saka shi a shafin sa na dandalin sada zumunta na Facebook a yau din nan.

.com dai ta samu cewa jarumin ya bayyana tun farko cewa shi dama can ba yaje wurin bane domin ya burge wasu ba yaje ne don yana ganin hakan ya dace a iya ilimin sa sannan kuma ya shawarci masu sukar maulidin da su je su nemi ilimi akan hakan don kuwa shi ilimi kogi ne. Daga karshe ne kuma dai sai jarumin ta bayyana cewa shi yafi son yayi murnar zagayowar ranar haihuwar fiyayyen halita Annabi Muhammadu fiye da yayi murnar zagayowar ta sa.

Share this


0 komentar:

Post a Comment

Popular post

No.1 Nigerian Blog || Free Download | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Design By Hausazone Technologies