Home

Music

Video

Kanny

Tags:

Babban jami'in Buhari ne ya bukaci mu ajiye naira biliyan 50 a bankuna – Inji shugaban NNPC


An zargi Abba Kyari a kan biliyan 50 da kamfanin NNPC ta ajiye a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA - NNPC ta umarni wasu bankunan kasuwanci don ci gaba da ajiye asusun a waje da TSA - Bankunan sun yi ikirarin cewa shugaban kasa ya amince da asusun Majalisar wakilai a ranar Talata, 12 ga watan Disamba ta gabatar da tambayoyi game da umarnin fadar shugaban kasa na riƙe wasu asusun ajiyar kamfanin albarkatun man fetur na kasa, NNPC daga mayar da ita zuwa asusun TSA. Majiyarmu ta tabbatar da cewar, asusun tana da naira biliyan 50 a cikin ta, wanda har yanzu tana watse a bankunan kasuwanci, wannan ya sabawa tsarin TSA, wanda ta bukaci cewa duk asusu na ma'aikatu da hukumomi na gwamnati a mayar da su zuwa asusun TSA. TSA wanda ita ne asusun ajiyar kudaden shiga na gwamnatin tarayya, kuma ta kasance a karkashin Babban Bankin Najeriya. Wani kwamiti na musamman na majalisar wanda dan majalisa daga jihar Kano, Alhaji Abubakar Danburam-Nuhu ya jagoranta ya gano cewa NNPC ta umarni wasu bankunan kasuwanci don ci gaba da ajiye asusun a waje da TSA. CBN ta tabbatar wa kwamitin cewa tana da masaniya game da asusun ajiyar kuɗi, yayin da ta nuna takardun shaida da NNPC ta bayar da cewa an samu amincewar shugaban kasa. Amincewar ta kushi a wata wasikar da shugaban ma’aikatan shugaban kasa, Abba Kyari ya rubuta, yana ba NNPC izini a kan ta cire asusun daga TSA. Da yake nuna takaici game da binciken, Danburam-Nuhu ya ce, "Bankunan har yanzu ta ci gaba da rike kudi har zuwa biliyan 50 a waje da TSA.

Share this


0 komentar:

Post a Comment

Popular post

No.1 Nigerian Blog || Free Download | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Design By Hausazone Technologies