Adam Zango yayi bukin kaddamar da sabuwar fim din sa mai suna gwasko a Kano - Jarumai kamar Ali Nuhu, Nafisa Abdullhi da Fati SU, sun halarci bukin - Zango ya karrama masoyansa da suka halarci bukin da kyaututtuka Shaharrren dan wasan kwaikwayon Kannywood Adam A Zango, ya karrama masoyan sa dake garin Kano a lokacin bukin shirrin kaddamar da sabuwar fim din sa mai suna gwaska Return da zai fito a ranar 1 ga watan Janairu na shekara 2018. Adam A zango yayiwa masoyansa da suka halarci bukin kyaututuka da ya kunshi riguna, huluna da sauran su. Jarumai kamar Ali Nuhu, Nafisa Abdullhi Fatu SU, sun halarci bukin a birnin Kano.


Daya daga cikin hadiman Zango, mai suna Mansur Make-Up, ya bayyana wa yan jarida cewa Adam Zango ya shirya bukin ne domin nuna ma masoyar sa irin kaunar da yake musu. Jaruma FatI Su ta shaidawa yan jarida cewa Adam Zango mutum ne mai matukar kaunar jama’a, kowa nasa ne, kuma abun da yayi wa masoyan sa abun ne da ya cancanci yabo ne. Mutum ne dake da matukar kyauta da taimako. Har mu ma jaruman fim bai bar mu wajen ganin cewa mun samu daukaka a masana’artar fim.
0 komentar:
Post a Comment