Home

Music

Video

Kanny

Tags:

Rikici kan budurwa ya tunzura wasu dalibai 3 sun kashe wani Mutum a Katsina



Jami'an rundunar yan sandan Jihar Katsina sun cafke wasu dalibai 3
- Kwamishinan yan sanda na Jihar, Benson Gwana ya bayyanawa wa manema labarai ana zargin su da aikata kisan kai
- An cafke daliban ne bayan sunyi wa mammacin rauni masu tsanani a dalilin wata budurwa da suke nema
Jami'an rundunar yan sandan Jihar Katsina sun cafke wasu dalibai 3 da ke karatu a Jami'ar Umaru Musa Yaradua da ke Katsina bisa laifin kashe wani bawan Allah mai sunanAbdulmalik Kabir kan wata mace da suke nema.
Kamar yadda Kwamishinan yan sanda na Jihar, Benson Gwana ya bayyanawa wa manema labarai a ranar Juma'a, daliban da ake zargi da aikata kisan kai duka maza ne, guda 2 na aji 3, shi kuma guda yana aji 2 duk dai a Jami'ar.
Jami'an yan sanda sun cafke daliban ne bayan sunyi wa mammacin rauni masu tsanani a dalilin wata budurwa da suke nema. An garzaya da mammacin asibiti inda yake karaban magani amma daga baya ya rasu a cikin watan Nuwamba.

Share this


0 komentar:

Post a Comment

Popular post

No.1 Nigerian Blog || Free Download | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Design By Hausazone Technologies