Majalisar Dinkin Duniya ta sanya Saudiyya a jerin kasashen da za ta fitar wadanda ke kashe yara a lokutan yaki, saboda rawar da take takawa a gamayyar da take jagoranta wajen yakin Yemen. Sanarwar da MDD ta fitar ta ce ayyukan gamayyar kasashen sun jawo mutuwar yara 638 a shekarar 2016, ta kuma zargi gamayyar da kai hare-hare 38 kan makarantu da asibitoci. Haka kuma MDD ta sanya dakarun gwamnatin Yemen, wadanda gamayyar ke jagoranta da kuma kungiyar Houthi a daftarin jerin wadanda suke kashe yara lokutan yaki. Sai dai gamayyar kawancen kasashen ta yi watsi da batun cewa tana sane take kai hare-hare kan fararen hula da kuma gine-gine. An kashe fiye da mutum 8,530, wadanda kashi 60% daga cikinsu fararen hula ne, kuma hare-haren sama sun jikkata mutum 48,800 tun daga watan Maris din 2015, a cewar MDD. Yakin na Yemen ya kuma bar mutum miliyan 20.7 cikin tsananin bukatar agajin gaggawa, al'amarin da ya jawo tsananin bukatar abinci da ba a taba ganin irin sa ba a duniya. A ko wacce shekara, sakataren MDD na fitar da rahoto kan yara da yake-yake wanda ke dauke da jerin sunaye na wasu bangarori da ake zargi da take hakki. Daftarin rahoton na baya-bayan nan na cewa: "A Yemen, ayyukan gamayyar kasashen da Saudiyya ke jagoranta ya jawo kashe yara har 638, kuma an samu wannan adadi ne bayan an tabbatar da cewa ita ke da alhakin kai hare-hare 38 a makarantu da asibitoci a shekarar 2016."

Su kuwa kungiyoyin Houthi da na al-Qaeda da dakarun da ke goyon bayan gwamnati wannan ne karo na biyu a jere da ake lissafa su a 'masu wannan laifi.' Haka kuma rahoton ya nuna karara cewa MDD ta yi amanna gamayyar kasashen 'ta fara daukar matakan da suka dace a lokacin da ake hada daftarin rahoton don tabbatar da bai wa yara kariya." Wakilin Saudiyya na dindindin a MDD, Abdallah al-Mouallimi, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa ba zai ce komai ba kan rahoton har sai sakataren Majalisar António Guterres, ya amince da shi a hukumance nan gaba cikin wannan watan na Oktoba. Sai dai a watan Agusta Saudiyya ta ce babu wani tabbaci da zai sa a sanya gamayyar kasashen da take jagoranta a jerin bangarorin da suke kisan yara a lokutan yaki. Shi ma mai magana da yawun MDD Stephane Dujarric ya ki cewa komai kan daftarin rahoton. Shugaban kungiyar Save The Children mai fafutukar kwatowa yara hakkokinsu Helle Thorning-Schmidt, ya ce, "Sakataren MDD ya yi abin da ya dace don kwatowa yaran da suke yankunan da ake yaki hakkokinsu. "Hakan zai sa duk bangarorin da aka sanya a wannan jeri da ma duk wani bangare da ke da hannu a yakin Yemen shiga taitayinsu, da ma kasashen da ke goyon bayansu da ba su makamai." A bara dai an cire gamayyar kasashen da Saudiyya ke jagoranta daga jerin sunayen da aka fitar na shekarar 2015, duk kuwa da korafin da kungiyar Save The Children ta yi.
0 komentar:
Post a Comment