Rundunar Yansanda jihar Abia ta bayyana cewa Sojojin Najeriya sun gano wasu bamabamai da sauran kayan fashewa a gidan shugaban kungiyar rajin kafa kasar Biyafara, IPOB. Jaridar The Nation ta ruwaito Kwamishinan Yansandan jihar Anthony Ogbizi yana bada tabbacin haka, inda yace a yanzu haka bama baman na hannun hukumar Yansandan. Kwamishinan ya bayyana haka ne yayin daya je kai rahoto ga shugaban Yansandan yankin kasashen Inyamurai, AIG Taiwo Lakanu a babban ofishin Yansanda dake Umuahia, inda ya shaida masa cewa an kai hari a ofishin Yansanda dake Ariaria, inda aka kashe shugaban ofishin.

Majiyar NAIJ ta ruwaito Kwamishinan yana fadin sun kama wasu yan kungiyar su 37, inda yace za’a gurfanar dasu a gaban kotu a ranar Talata 19 ga watan Satumba.Talatin daga cikinsu an kama su ne a garin Isiala Ngwa, sauran bakwan kuma an kama su da hannu cikin babbaka ofishin Yansandan. “Mutanen nan sun kai hari har gidan mataimakin sufeton Yansanda na kasa dake shiyya ta 9, da kuma gidan kwamishinan Yansandan jihar. Kuma duk daga gidan shugaban IPOB din suke fitowa da makamai da bamabaman da suke amfani dasu.” Inji shi.
0 komentar:
Post a Comment