Home

Music

Video

Kanny

Tags:

WAI SHI DAN JAM'IYYAR APC WALIYINE KODA YA KWASHE SHEKARU 12 A CIKIN JAM'IYYAR PDP?- in ji Jonathan


A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook, tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya ce munafunci irin na 'yan jam'iyyar APC ne ya sanya mutane irinsu Sanata George Akume suka ce PDP ce ta jefa kasar cikin mawuyacin halin da take ciki. "Sanata Akume (dan majalisar dattawa na jam'iyyar APC) kamar Mallam Bolaji Abdullahi (tsohon minista a gwamnatin Jonathan), ya manta cewa PDP ta yi mulkin shekara 16 kuma Akume ya zama gwamna karkashin Jam'iyyar PDP na shekara takwas, kana ya zama sanata a karkashinta shekara hudu. Tsohon shugaban kasar ya yi raddi ne kan kalaman da aka ambato kakakin jam'iyyar APC Mallam Bolaji Abdullahi ya yi cewa babu wanda ya sace kudin Najeriya kamar Mr Jonathan da kuma wanda Mr Akume ya yi cewa PDP ce ta jefa kasar cikin bala'in talauci. Ko menene Ra'ayin ku a kan wannan dambaruwa?

Share this


0 komentar:

Post a Comment

Popular post

No.1 Nigerian Blog || Free Download | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Design By Hausazone Technologies