Home

Music

Video

Kanny

Tags:

Rundunar 'Yan sanda Ta Zargi Kwankwasiyya Ta Haddasa Rikicin Kano


Rundunar 'Yan sandan jihar Kano ta zargi magoya bayan akidar Kwankwasiyya da haddasa rikicin siyasa a jihar wanda ya yi sanadiyyar mutane da dama suka samu raunuka a makon da ya gabata. Kwamishinan 'Yan sandan jihar, Rabi'u Yusuf ya ce magoya bayan Kwankwasiyya daga jihohin Sokoto, Kogi da wasu makwaftan jihohi sun yi wani gangami a Asibitin Hasiya Bayero da nufin tarwatsa Hawan Daushe wanda masarautar Kano ke shirya a duk shekara, lamarin da ya janyo arangama da magoya bayan Gwamnan Jihar, Umar Ganduje.

-Rariya

Share this


0 komentar:

Post a Comment

Popular post

No.1 Nigerian Blog || Free Download | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Design By Hausazone Technologies