Home

Music

Video

Kanny

Tags:

Mutanen da suka yi alkawarin taimaka ma Asibiti na da kudi sun guje ne bayan rasuwar Yar’adua – Turai


Uwargidar tsohon shugaban kasa Alhaji Umaru Musa Yar’adua, Hajiya Turai Yar’adua ta bayyana dalilin daya sat a gagara kammala aikin katafaren cibiyar kulawa da masu cutar daji, wato Cancer. Daily Trust ruwaito Turai Yar’adua na fadin cewa ta gagara kammala aikin ne saboda bayan rasuwar mijinta, duk wadanda suka yi alkawarin bada taimakon suka ki bayarwa.

Turai ta bayyana haka ne yayin da daliban Najeriya mazauna kasar Uganda suka kai mata ziyara suka bata kyautar girmamawa a Abuja, karkashin jagorancin shugabansu Mubarak Yahaya Adamu.

Babban burina shine in kammala gina cibiyar kafin mijina ya rasu, saboda har mun ti taron tara kudaden yin aikin asibitin, amma da mijina ya rasu, sai duk mutanen da suka yi min alkawarin taimaka min da kudaden suka ki bayarwa. “Saukin ta ma mun kammala kashin farko na asibitin, muna sa ran zuwa shekarar 2018 zamu kammala aikin ginin asibitin. Don haka nema zamu samu wani mutumi da yayi fama da cutar daji, mu bashi shugaban hukumar gudanarwar asibitin. ” Inji ta Turai Yar’adua tace da zarar ta kammala gina asibitin, tana sa ran har daga kasar waje za’a dinga zuwa asbitin, sa’annan zata dinga daukan nauyin mutanen da ba zasu iya biyan kudin da kansu ba. A nasa bangaren, shugaban kungiyar daliban, Adamu yace sun ga dacewar baiwa Turai Yar’adua lambar girmamawar ne sakamakon kokarin da take yi wajen inganta rayuwar gajiyayyu.

Share this


0 komentar:

Post a Comment

Popular post

No.1 Nigerian Blog || Free Download | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Design By Hausazone Technologies