Ministan wasanni da harkokin matasa na kasa, Barrister Solomon Dalung, ya wallafa a shafin sa na sada zumunta yadda har yanzu bai saki tsohuwar al'ada da tsofin abokan arziki ba duk da kasancewar sa minista mai ci. Ga abinda ya ce; Shan shayi da abokanan arziki a Jere hanyan Kaduna. Kyakyawan zaman tare ita ce waiwaiya kana hada kai da nuna kauna wa duk al'uma ta kowace hali. Ko ana mulki ko babu mulki, mu'amula da abokanan arziki da kiwaye ya zama dole. Wannna ita ce hakin mu shugabanai. Allah ya sa mu dace. Amin







0 komentar:
Post a Comment