Home

Music

Video

Kanny

Tags:

Mawaka sun Nuna bacin ransu akan Nadin Korade Bello


Mawakan Arewacin Nigeria sun Nuna Rashin jin dadinsu akan Nadin da masarautar Kano tayi ma mawakin kudancin Nigeria Korede Bello a matsayin SARKIN WAKA, suna ganin hakan kamar wani cin mutunci ne, wanda ana amfani dasu ne kawai lokacin da zasuyi amafani idan ya wuce a watsar dasu. Gadai abinda wani Shahararren Director FALALU A DORAYI ya rubuta a shafinsa na Instagram Wanda ya samu goyon baya daga wajen mawaka da yawa Irinsu Adm A Zango, Umar m shareef, Abdul D One, Ado Gwanja, Nazeer M Saulawa da dai sauransu. Ga abinda ya rubuta. " NA DADE DA GANE CEWA MAWAKAN AREWA GYANDIR NE!! MU HANKALTA KO MU WULAKANTA..... Zanyi tsokaci akan Hutunan da suke sama. Duk da dai ba halina bane shiga sabgar mutane. Ina magana ne akan nadin Sarautar SARKIN WAKA da ake cewa an yi wa wani mawakin kudu KOREDE BELLO a Kano. In ta tabbata kamar yadda mawakin ya wallafa a page dinsa.. To lallai mawakan hausa na Arewa sai addua. Nasan duk rashin basirar Mawakanmu ba suyi Lalacewar da sai an tsallaka Lagos za'a samo musu Sarki ba. Koda yake ba abin mamaki bane dama haka manyan Arewan namu suke, lokacin bukatarsu suke nemanmu, lokacin moriyar sai dai mu gani a wajan yan kudu. Ina mamakin yadda ciki yake manta kyautar jiya. Duk wahalar da mawaka kiyi akan masu kudi, masu Sarauta, da Yan siyasa na Arewa wajan yi musu wakokin yabo da kwarzantasu abin takaici sai kaga babu wani lada. Tun da aka nada Sarkin kano na Yanxu Dan maje, Nazir Sarkin Waka ya sashi a gaba da yabo da kirari a cikin wakenma akwai inda ya hararomasa zama Sarkin kano, kuma Allah da ikonsa ta tabbata.... Bayan ya zama Sarkin Kano bai bar wake shi ba har gobe. Kuma in zaayi adalci a duk wakokin da akaiwa Sarkin kano banajin akwai wadda ta kai ta Nazir Ahmad Tasiri.

Tabbas nazir yafi Korede bello cancantar sarautar duk da bamu san irin kalaman da Korede ya zuba a wakar da yaiwa Sarkin ba.. Sarautar waka a garin hausawa sai mai jin hausa, a tsallake a dauko wani ko hausa cikakkiya ba ya ji, bai taba yin Waka da hausa ba, bai yiwa kano da Kanawa ko baiti daya ba, bai yiwa Sarkin kano waka ba, a bashi wannan mukami? Shikenan anci yaki an barmu da kuturun bawa. A bayyane yake mafi yawan manyanmu na Arewa suna mutunta ra'ayin Yayansu ne kawai, su kuma Yayan nasu ba su girma a kasar ba ma, ba su damu da komai na hausa da Al'ada ba, Wannan yasa Biki, suna, bthday, murnar kammala karatu, baiko da duk wani abin murna Mawakan kudu ake daukowa su baje kolinsu. In aka ce su dauko mawakan arewa sai suce Yan kauye ne.

Idan har Nazir bai zama Sarkin Mawakan Sarkin Kano ba to banga Wanda ya kaishi ba. Ku girmama al'ummar ku sai wata al'ummar ta girmama ta. Ni nasan dan kudinku da kudin yayanku suke zuwa sabgarku.

Share this


0 komentar:

Post a Comment

Popular post

No.1 Nigerian Blog || Free Download | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Design By Hausazone Technologies