Wasu dumbin mata daga Kungiyar 'yan uwa Musulmi wadda aka fi sani da Shi'a a Nigeria, sun bukaci hukumomi a kasar da su gaggauta sakin Shugabansu Sheikh Ibrahim El-Zakzaky. Matan wadanda suka gudanar da zanga-zanga a ranar Laraba a habarar hukumar kare hakkin bil'adama da ke Abuja, sun ce sau da dama kotu a kasar na bayar da umarnin a saki Sheikh El-Zakzaky amma har yanzu gwamnatin kasar ta ki yin biyayya ga hukuncin kotun.
0 komentar:
Post a Comment