Ga duk mai bibiyar harkokin masana’antar shirya finafinan Hausa watau Kannywood, ya kwana da sanin bullar sabuwar jaruma Maryam Yahaya (Mansoor), wadda za a iya cewa ta shigo farfajiyar fim da kafar dama, kasancewar ta zamo cikin jerin taurarun da ake sa ran za su haska nan da shekaru masu zuwa. Akwai mamaki matuka yadda cikin lokaci kankani lokaci jarumar ta yi wa takwarorinta fintikau wajen yawan fitowa a finafinai masu kyawun gaske, ko da yake ba abin mamaki ba ne idan aka yi la’akari da kamfanin FKD Production da ya tsaya tsayin daka wajen yi mata babban fim watau MANSOOR, wanda aka saki a satin karamar Sallah a sinimun da ke fadin kasar nan, ranar 30 ga watan Yuni 2017. Ga jerin fina-finan da jarumar ta fito cikinsu da suka hada da: Tabo, Mijin Yarinya, Adamun Adama, ‘Yar Me Ganye, Duhun So, Arashi da dai sauransu. Mujallar muryar talaka





0 komentar:
Post a Comment