Home

Music

Video

Kanny

Tags:

EFCC ta gano $1.5 biliyan a cikin wani asusun Diezani na kasar Switzerland


Labaran da muke samu yanzu ba da dadewa ba daga majiyoyin mu da dama na nuni da cewa hukumar nan dake yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta sake bankado wata badakala ta makudan kudaden da suka kai dalar amurka biliyan 1.5 a cikin wani asusun da ke da alaka da tsohuwar ministar mai Diezani Alison Madueke. Hukumar dai ta EFC tace a dan binciken da ta fara ta gano cewa asusun bankin yana da alaka ne da ita tsohuwar ministar da kuma wasu manyan jami'an gwamnati abokanta su hudu kuma sun samu kudin ne bayan sun saida wani bakin man kasar. Majiyarmu haka ma dai ta samu cewa fadar shugaban kasar Najeriya ta yi kaca-kaca da wata tsohuwar ministar tsohon shugaban kasar Najeriya Obasanjo kuma shugabar kungiyar nan dake fafutukar ganin an sako yan matan Chibok daga kungiyar Boko Haram mai suna Uwargida Oby Ezekwesili. Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwar da mai taimakawa shugaba Buhari ta hanyar yada labarai Malam Garba Shehu ya fitar inda ya shawarci tsohuwar Ministar da ta sa kunya a ranta ko da sau daya ne ta yi tofin Allah-tsine ga yan uwanta masu fafutukar ganin sun kafa kasar Biyafara.

Naijhausa

Share this


0 komentar:

Post a Comment

Popular post

No.1 Nigerian Blog || Free Download | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Design By Hausazone Technologies