Home

Music

Video

Kanny

Tags:

CACOL ta lissafo ministoci 4 da ya zama dole Buhari ya dakatar da su


Kungiyar CACOL tayi kira ga gwamnatin Buhari da ta tsige wasu ministoci - Kungiyar ta zargi ministocin da rashin kokari kamar yadda ya kamata - Sun kuma bukaci shugabna kasa da ya bar kujerar a matsayin ministar man fetur Kungiyar dake yaki da cin hanci da rahaswa ta CACOL tayi kira ga shugabna kasa Muhammadu Buhari da ya tsige wasu daga cikin ministocin sa. A wata sanarwa daga shugaban kungiyar, Debo Adeniran, kungiyar ta lisaffo wasu ministoci wanda suke ganin basu tabuka wani abun kirkiba sannan sun yi kira ga a tsige su. Musamman CACOL ta ambaci Babatunde Fashola, ministan wutar lantarki da gidaje, inda suka bayyana cewa ya gaza aikin sa. Sun kuma yi kira ga shugaba Buhari da ya sauka a matsayin ministan man fetur saboda ya maida hankali a al’amuran dake damun kasar. Daga karshe sun nemi a sauke ministan shari’a, Abubakar Malami da kuma kudi Misis Kemi Adeosun a cewarsu dukkansu sun gaza a kan ayyukan su.

Share this


0 komentar:

Post a Comment

Popular post

No.1 Nigerian Blog || Free Download | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Design By Hausazone Technologies