Cikin kayayyakin da Faston ya rabar sun hada da lemun kwalabe, sabulai da kuma abinci, inda yace yayi haka ne don cika manufarsa na taimaka Musulmai gajiyayyu don su samu walwala a yayin bukukuwan Sallah. Daga karshe Buru ya bukaci da ya dace a inganta dangataka tsakanin mabiya addinin Musulunci da na Kirista, inda yace dukkanin mabiya addinan yan uwan juna ne. Majiyarmu ta ruwaito shugaban gajiyayyun, Muntari Saleh ya gode ma Faston, kuma yayi addu’ar Allah ya saka masa da alheri.





0 komentar:
Post a Comment