Home

Music

Video

Kanny

Tags:

Ta yiwa mijinta barazanar yanke ma sa mazakuta don haka ya na neman kotu ta raba auren su


Ta yiwa mijinta barazanar yanke ma sa mazakuta don haka ya na neman kotu ta raba auren su A can jihar Kwara kuma, wani mutum yana rokon kotu da ta raba aure dake tsakanin sa da matar sa domin ta yi masa barazanar yanke ma sa mazakuta A ranar Larabar da ta gabata ne, wani mutum a jihar Ilori ya roki wata kotu da ta raba auren sa da matar shi domin yana jin tsoro akan barazanar yanke ma sa mazakuta da ta yi. Fatahi Zakariya'u, ya zayyanawa kotu cewa, matar sa Ganiyat ta dauki hali da at ke yi masa barzanar yanka mazakutansa a duk lokacin da suka samu wata 'yar hatsaniya a tsakanin su. Ya ce gwara kotu ta raba auren su tun kafin a je ko ina kuma daman akwai lokacin da ta taba sanya ma sa guba a cikin abinci sa. Ya ce, "ya mai shari'a, ina so a raba auren mu domin abu kadan zai yi sai matar sa ta hayayyako ma sa da fada kuma ta na yi ma sa barazanar yanke ma sa mazakuta a kowane lokaci da hakan ya faru." Ta na yawan fada da makota kuma a gaskiya bazan juri zama da wacca ba ta kare mutuncin kan ta ba kuma tabbas ina shayin ta domin kuwa na taba cafke ta tana zuba guba acikin abinci na kuma akwai ta da ziyartar dan duba." Ita kuwa Ganiyat, ta nemi agajin kotu da ta roki mijinta akan kar a raba aurensu kuma tayi alkawarin za ta sauya dabi'un ta da managarta domin har yanzu tana matukar kaunar sa kuma ba ta da niyyar rabuwa da shi. Alkali mai shari'a, Abdulkadir Ibrahim, ya baiwa wannan ma'aurata shawara da su kara hakuri da juna don wata kila za su iya fuskantar juna, kuma da wannan ne ya daga sauraron karar zuwa ranar 19 ga watan Satumba domin cigaba da shari'a.

Share this


0 komentar:

Post a Comment

Popular post

No.1 Nigerian Blog || Free Download | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Design By Hausazone Technologies