Mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II ya bukaci masu hannu da shuni dasu dinga taimaka ma al’umma da arzikin da Allah yayi musu, musamman ma matasa. Kamfanin dillancin labaran Najeriya, NAN, ta ruwaito Sarkin na yin wannan kira ne a ranar Talata 22 ga watan Agusta yayin taron wata kungiyar likitoci, NSHBT daya gudana jihar Kano.
Sarkin yace yayi wannan kira ne sakamakon yadda al’umma ta lalace, jama’a basu taimakon juna, don haka ne yaga dacewar masu hanndu d shuni su dinga taimaka ma matasa a sha’anin karatu, musamman talakawa.
Majiyar NAIJ.com ta ruwaito ta ruwaito Sarkin ya nuna farin cikinsa game da yadda dan jihar Kano ne ya gabatar da kasida a yayin taron, wato Farfesa Abba Zubair, wanda shine shugaban cibiyar kula a ciwon sikila ta Mayor Clinic dake jihar Florida, kasar Amurka. Sarki yace ilimi shine kadai abinda iyaye zasu iya barin ma yayansu, sa’annan ya yaba ma mashirya taron, kuma ya baiwa kungiyar kyautan naira miliyan daya. shima shugaban kungiyar, Farfesa Sulaiman Akanmu yace zasu cigaba da bada gudunmuwa waje maganin cutar Sikila. A nasa jawabin, Gwamna Abdullahi Ganduje, wanda ya samu wakilcin shugaban hukumar yaki da cutar sida ta jihar Kano, Dakta Usman Bashir yace gwamnatin jihar Kano ya kashe naira biliyan 5 wajen samar da kayan aiki a asibitocin Giginyi dana Zoo road.





0 komentar:
Post a Comment