Home

Music

Video

Kanny

Tags:

Jerin sunayen Mutane biyar da sukaji kunya bayan dawowar shugaba Buhari

- Wasu sun ji kunya da dawowar Shugaba Muhammadu Buhari - Akwai wadanda su ka rantse Shugaban kasar ba zai dawo ba - Daga cikin akwai irin su Gwamnan Jihar Ekiti Ayo Fayose Ba shakka wannan shi ne abin da Bahaushe yake cewa Marada sun sha kunya. Wasu sun rantse cewa Shugaba Buhari ba zai dawo Ofis ba sai ga shi ya dawo. Daga cikin wadannan jama'a ko mutane akwai:

Read more: Cikakken Jawabin shugaba Buhari zuwa GA yan nigeria

1.Gwannan Jihar Ekiti Gwamna Ayo Fayose na Jihar Ekiti ya rantse cewa Shugaba Buhari yana can rai hannun Allah a Landan har yayi ikirarin yana da hotunan sa. Sai ga shi ashe ba haka abin yake ba.

2.Femi Fani-Kayode

Tsohon Ministan kasar Femi Fani-Kayode yana cikin wadanda su kace Shugaban kasar ba zai dawo ba. Shi ma dai ya ga ikon Allah.

3. Nnamdi Kanu Shugaban tafiyar Biyafara Nnamdi Kanu a baya yace ta Shugaba Buhari ta kare don ya gama mulki. Kamar dai yadda Babban Faston Ingila J. Welby ya fada addua tayi aiki.

4. 'Yan Shia Ana zargin 'Yan Shia da yi wa Shugaban kasar asiri. Wani Dan Majalisa da kan sa ya bayyana wannan kwanakin baya. Wasun su dai sun sha alwashin Shugaban kasar ba zai dawo ba.

5. Sauran Jama'a Jaridar Washington Post ta Amurka dai tayi kokarin bayyana haka a wani rubutu inda ta kawo abin da ya faru da Marigayi Shugaba 'Yaradua.

Share this


0 komentar:

Post a Comment

Popular post

No.1 Nigerian Blog || Free Download | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Design By Hausazone Technologies