Home

Music

Video

Kanny

Tags:

Dawowar Shugaba Buhari; Ji me Asari Dokubo ke cewa cikin shagube

Dawowar Shugaba Buhari; Ji me Asari Dokubo ke cewa cikin shagube

- Mujadihi Asari Dokubo, dan raji da babatun kare hakkin yankin kudancin Najeriya ne, wanda tun zamanin mulkin Obasanjo yake karadi da cika baki kan lallai sai ya kori gwamnatin tarayya daga cin arzikin yankinsu mai arzikin man fetur. Bayan dawowar shugaba Buhari a jiya, masu tsokaci sun bude kaafensu domin yabawa, murna ko suka da nuna bakin cikinsu. Asari Dokubo ma dai bai bari an barshi a baya ba, ya nadi bidiyo inda yake caccakar magoya bayan Buhari da ma shugaban.

Asari Dokubo ya ce mutane su dena damun jama'a da wata murnar wai Baba ya dawo, amma su nuna fushinsu kan kin gayawa mutan kasar nan cutar da ke damunsa da Buharin yayi.
Ya kuma yi kira ga shugaba Buhari da ya dena boye-boye kan rashin lafiyar tashi, sannan yace shugaban yayi wa jama'a aikin da suka zabo shi yayi.

-Naij

Share this


0 komentar:

Post a Comment

Popular post

No.1 Nigerian Blog || Free Download | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Design By Hausazone Technologies