An kaddamar da wani malami a kotu bayan an zarge shi da yin lalata da 'yan uwa 3

An kaddamar da wani malamin Larabci,mai suna Ibrahim Idris shekaru 23, a ranar Talata a wata Kotun Majistare ta Ikeja, wanda ake zargin yayi lalata da 'yan mata uku. Wadannan 'yan matan da ake zargin anyi lalata dasu sun kasance 'yan uwan juna.Suna zaune ne a 2, Kelani st Adealu bus, a wata yankin Dopemu a Legas. Ana kaddamar da bincike akan mutumin da ake tuhuma don gurfanar da shi. Mai gabatar da kara, Insp. Clifford Ogu, ya shaida wa kotun cewa wanda ake tuhuma ya aikata laifin ne daga watan Mayu zuwa Agusta, 2017, a gidan shi. Ogu ya ce 'yan uwa ukun, wadanda shekarunsu suka kasance daga shekaru bakwai zuwa shekaru 12, suna koyon harshen Larabci da Ilimin Islama daga wanda ake zargi. "Iyayen ba su san cewa wanda ake tuhuma yana cin zarafin 'ya'yansu mata ba sai da suka canza gida kuma suna buƙatar canza makarantar Larabci na yaran." "Mafi karaman yarinyar ta shaida wa mahaifiyar cewa ba ta son wani malami ya koya musu," in ji shi. Ogu ya kara da cewa bayan ta ji maganganun 'yarta, mahaifiyar ta yi tambayoyi kuma su ka gaya mata abin da malamin yake yi musu. "An bayar da rahoton ne a ofishin 'yan sanda, kuma aka kama wanda ake zargi," in ji shi. A cewarsa,laifin ya saba wa sashe na 137 na dokar laifuka na Jihar Legas, 2015. Amma wanda ake zargi ya ki yarda da laifin da ake tuhumarsa akai. Babbar majistare, Mrs Taiwo Akanni, ta amince wa wanda ake zargin belin N250,000, tare da shaidu guda biyu da adadin kuɗin. Akanni ta dakatar da shari'ar har sai ranar 11 ga watan Satumba (NAN). -Naij
0 komentar:
Post a Comment