'Yan uwan marigayi Laftanar Kanar Muhammad Abu Ali,
kwamandan rundunar sojin kasar ta 272 mai kula da
tankokin yaki, da 'yan Boko Haram suka kashe a jihar
Bornon Najeriya sun zargi rundunar sojin kasar da rashin ba
shi hutu.
Amina Abu Ali, kanwar Muhammad Abu Ali, ce ta yi wannan
koke lokacin da wata kungiya mai rajin kare hakkokin sojin Najeriya
da suka rasa rayukansu a lokutan yaki ta je yi musu ta'aziyya a
Kaduna.
A cewarta, "Muna fatan sojin Najeriya za ta kammala yaki da 'yan
Boko Haram domin gudun ci gaba da asarar zaratan sojin kasar".
Ta kara da cewa ya kamata a canza lokacin da sojoji ke shafewa a
fagen daga domin "idan sun dade a can akwai gajiya. Sojoji na nan
ko'ina, ba wai wasu sojoji ne kawai za su yi wannan yakin ba".
Ta ce "Dan uwana ya zauna a Maiduguri tsawon shekara biyu,
amma hutun mako biyu kawai aka ba shi."
BBC ta tuntubi Kakakin rundunar sojin kasa kan wannan zargi,
amma har yanzu ba mu samu amsa ba.
A ranar Litinin din da ta gabata ne aka yi jana'izar Muhammad
Abu Ali tare da wasu sojoji hudu.
Sun mutu ne lokacin da suke kokarin dakile wani harin da mayakan
kungiyar Boko Haram suka kai a barikin sojin kasar na 119 da ke
garin Malam Fatori a jihar Borno.
Kafin rasuwarsa, Kanar Ali ya taka rawa sosai wurin kwato wasu
garuruwa daga hannun Boko Haram, abin da ya sa aka yi masa
karin girma.
Baya ga iyalan Kanar Ali, sojoji da dama da ke fafatawa a yankin
Arewa maso Gabas, na kokawa kan rashin musanya su da karancin
samun hutu.
Source:- BBCHAUSA
'Yan uwan Kanar Abu Ali sun zargi sojin Nigeria
Share this
|
|





0 komentar:
Post a Comment