A Najeriya, kamfanin man kasar, wato NNPC ya sake
komawa yankin Chadi don ci gaba da bincike da nufin gano
ainihin adadin mai da iskar gas din da ke karkashin kasa a
yankin.
A wata hira da BBC, shugaban kamfanin man Najeriya, Dr
Maikanti Baru, ya ce NNPC zai yi amfani da wasu manyan
na`urori wajen yin binciken.
Ya kara da cewa idan har abun da aka samu ya kai wani mizani, to
kamfanin zai dukufa wajen hakar man.
Tun a shekarun 1970 ne wasu masana da kuma kamfanin NNPC
suka yi hasashen cewa za a iya samun mai a yankin, kuma tun daga
wancan lokacin aka yi yunkuri daban-daban don binciken man amma
ana dakatarwa saboda wasu dalilai, ciki har da zargin cewa akwai
siyasa a cikin lamarin.
[Labari] NNPC na ci gaba da binciken mai a arewacin Nigeria
Share this
|
|





0 komentar:
Post a Comment